2 Timothy 3

Rashin Sanin Allah a Kwanakin Ƙarshe

1Amma fa ka san wannan: Za a yi lokatan shan wahala a kwanakin ƙarshe. 2Mutane za su zama masu son kansu, masu son kuɗi, masu taƙama, masu girmankai, masu zage-zage, marasa biyayya ga iyayensu, marasa godiya, marasa tsarki, 3marasa ƙauna, marasa gafartawa, masu ɓata sunayen waɗansu, marasa kamunkai, masu ƙeta, marasa ƙaunar nagarta, 4masu cin amana, marasa hankali, waɗanda sun cika da ɗaga kai, masu son jin daɗin a maimakon ƙaunar Allah—  5suna riƙe da siffofin ibada, amma suna mūsun ikonta. Kada wani abu yǎ haɗa ka da su.

6Irin su ne suke saɗaɗawa su shiga gidaje suna rinjayar mata marasa ƙarfin hali, waɗanda zunubai suka sha kansu, mugayen shaʼawace-shaʼawace kuma sun ɗauke hankulansu, 7kullum suna koyo amma ba sa taɓa iya yarda da gaskiya. 8Kamar dai yadda Yannes da Yamberes
Yannes da Yamberes: Babu waɗannan sunaye a Tsohon Alkawari, amma bisa ga masanan tarihin Yahudawa, mutanen nan su ne bokayen nan biyu na ƙasar Masar da suka yi gāba da Musa lokacin da ya so yǎ fitar da ʼyaʼyan Israʼila daga ƙasar Masar (Dubi Fit 7.11, 22; 9.11).
suka tayar wa Musa, haka waɗannan mutane ma suke tayar wa gaskiya-mutane masu ɓataccen hankali, waɗanda, in ana zancen bangaskiya ne, to, fa ba sa ciki.
9Sai dai ba za su yi nisa ba, don rashin hankalinsu zai bayyana ga kowa, kamar na mutanen nan biyu.

Umarnin Bulus ga Timoti

10Kai kam, ka san kome game da koyarwata, da halina, da niyyata, bangaskiya, haƙuri, ƙauna, jimiri, 11tsanani, shan wahala-irin abubuwan da suka faru da ni a Antiyok, Ikoniyum da kuma Listira, tsananin da na jure. Duk da haka Ubangiji ya cece ni daga dukansu. 12Labudda, duk masu niyyar zaman tsarkaka, suna na Kiristi Yesu, za su sha tsanani. 13Mugayen mutane da masu ruɗi kuwa, ƙara muni za su riƙa yi, suna yaudara, ana kuma yaudararsu. 14Amma kai kam, ka ci gaba da abin da ka koya ka kuma tabbatar, gama ka san waɗanda ka koye su daga gare su, 15da kuma yadda tun kana ɗan jinjiri ka san Nassosi masu tsarki, waɗanda suke iya sa ka zama mai hikima zuwa ceto ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu. 16Dukan Nassi numfashin Allah ne yana kuma da amfani don koyarwa, tsautarwa, gyara da kuma horarwa cikin adalci, 17domin mutumin Allah yǎ zama shiryayye sosai saboda kowane kyakkyawan aiki.

Copyright information for HauSRK